DALILAI 13 DA KE SA NAMIJI KARA AURE



 Akwai dalilai da dama da su kan sa namiji ya yi wa matarsa kanwa, ko in ce abokiyar zama, zan fadi wasu daga ciki kamar haka: 

So da yawan lokacimata su ke ja har mijin su ya kara aure ta wajen rashin kula,  da tsaftar jiki, Muhalli kayan sawa da sauransu, wani kuma yana da aure-aure, haka kuma wani sunnar fiyeyyen halitta ya ke bi, ta haka ne wasu ke kara aure.

1.     Sakacin matargida: Wani kan yi wa matarsa kanwa ne sakamakon ita ba ta iya kintsa kanta ba, ballantana shi maigidan ko gidan ba, ba ta san yadda za ta adana shi ba, ba ta san yadda za ta sa maigida ya ji yana da mata ba, ballantana ya fahimci banbancinsa da tuzurai.
2.     Rashin wadatuwa da mace daya: Wani ya kan kara wa matarsa kanwa sakamakon karfin da yake da shi ta yadda ita kadai ba za ta iya jure tsananin bukatarsa ba.
3.      Bibiyar ‘yan tsibbu da bokaye:  Wani kan yi wa matarsa abokiyar zama ne sakamakon nacin matar da ya karo na bibiyar ‘yan tsibbu da bokaye har ta ja hankalinsa, kuma wata kila ta yi hakan ne domin kokarin shiga wata daula, ko hassadar ta ga matarsa ta farko.
4.     Jin dadin zama: Wani saboda jin dadin zama da kuma gamsuwa da halin matarsa kan sa ya karo mata abokiyar zama, domin hakan yana nufin cewa ya fahimci rayuwar aure akwai dadi, don dadinta ne ma har yake neman kari, tun da sai zama yayi dadi za ka dada kwadayin samun karin irinsa. 
5.     Rashin jin dadin zama da matar da suke tare: Wani kan samu matarsa mai bakin hali mara biyayya gare shi, hakan kan saka shi kokarin samo mata abokiyar zama, domin yana tunanin zuwanta na iya canza halin ta gidan, ko kuma yin hakan kan ba shi damar dandana dadin rayuwar aure, kamar yadda wasu mazan suke samu.
6.      Hukuncin kaddara: Wani kan yi wa matarsa kanwa ne saboda daman can Allah ya kaddara cewa ita ma dayar ko biyun ko ukun matansa ne.
7.     Cika tsohon alkawari: Wani kan yi wa matarsa kanwa ne saboda matar da zai karo tsohuwar masoyiyarsa ce da wani dalili ya hana ya aure ta, yanzu kuma wancan dalilin da ya hana ya kau.
8.     Sha'awa da gamon jini: Wani kan yi wa matarsa kanwa ne saboda ya sake ganin wata da ya yi shaawarta, jini ya hadu, kuma kauna ta shiga tsakani sai aka samu daidaito.
9.      Kwadayin samun haihuwa ko ‘ya’ya da yawa: Wani kan kara wa matarsa kanwa ne, ko dai saboda ita ba mai haihuwa ba ce, shi kuma yana son haihuwar, ko tana haihuwar amma shi kuma yana kwadayin ‘ya’ya da dama. 
10.      Huce haushi/takaici: Wani kan yi wa matarsa kanwa ne saboda ya huce haushin da matar tasa take kuntuka masa, ko kuma daman auren dole aka yi masa ba sonta yake yi ba, mai yiwuwa yana zaune ne da ita domin biyayya ga magabata, hakan tasa yake kokarin yin wani auren na soyayya, domin ya huce takaici. 
11. Nufin taimako/Kwadayin samun lada: Wani kan yi wa matarsa kanwa ne sakamakon kyakkyawar niyyarsa ta taimaka wa ta biyun, mai yiwuwa ko uwar marayu ce, ko ita din marainiya ce, ko kuma ya fahimci iyayenta na bukatar taimako. 
12. Amsa kokwan bara: Wani ya kan yi wa matarsa kanwa ne sakamakon kokwan bara da ta biyun ta kaddamar masa, shi ma kuma Allah ya karkato da zuciyarsa zuwa gare ta, daga nan kuma maganar aure ta kullu tsakaninsu.
13. Kisisina: Wani ya kan yi wa matarsa kanwa ne sakamakon iya kisisina na wacce ya karo, har ta iya jan hankalinsa ta shige ransa, daga karshe ya mace a kanta har ya aure tabbata a tsakaninsu.


 Wadannan abubuwan da aka zayyana a sama kan zamo dalilai da namiji yake iya karo wa matarsa abokiyar zama, duk da cewa za a iya samun wadansu ka iya haura wadannan ma yawa, amma dai zan so in takaita a kansu, ko wani ma ya samu abin fada. Kishiya yar’uwa ce kuma alkairi ce idan ka yi sa’ar ta gari.

 Karin auren maza wani abu ne da babu macen da za ta iya kauce masa ko ture sa in Allah ya kaddara sai an yi shi. Komin kuwa biyayyarta, soyayyarta da kuma yawan tattalinta.

 Karin aurensa ba yana nuna ya dai na son uwar ‘ya’yansa, ko kuma wacce zai dauko ta fita ba ne.

 A’a, tana nan a matsayin masoyiyarsa abar kaunarsa. 
Amma fa in ita ma ba ta canza a kan halayenta na gari ba.
 Haka ne kuma babu karya, kishiya aba ce mai zafi. 
Abun da nauyi a ce za ka fara raba masoyinka da wata. 

To amma wadannan jarabawowin mu ne mata, kuma ko wane jarabawa akwai alkairin da ka iya zuwa da shi. 

Kishiya ta gari tana iya taimakawa mace wajen ganin sun tafiyar da gidan mijinsu yanda ya dace. Kuma tana zuwa ne cikin gidanki da wasu kariya da za ta baki, ‘ya’yanki da kuma mijinki. 

Allah ya sa dukkan mata su fara daukar kishiya a matsayin abokiyar zama ta alkairi, amin.



Post a Comment

0 Comments