AMFANIN TAFARNUWA DAN KARIYA DA KUMA INGANTA LAFIYAR DAN ADAM.


Assalamu alaikum,barka da sallah da kuma sake saduwa daku a inda Allah a cikin ikonsa nine mai wannan shafin na " CIWO DA MAGANI " a yau na sake dawo maku da amfanin tafarnuwa dan samun kariya daga wasu cutuka na kwayar cuta ta Viral,bacterial da kuma fungal da kuma baiwa jiki damar samun ingantattar lafiya(sound health).

Ita dai tafarnuwa an fara amfani da ita a yankin Asiya ta tsakiya kimanin shekarru dubu biyar zuwa shidda da suka gabata,haka kuma ana amfani da ita a bangaren abinci da kuma sarrafa magani (for diet and drugs).A yanzu ana amfani da ita a yankin gabas ta tsakiya da kuma Afirika da nahiyar turai.

Tafarnuwa nada dubban amfani wanda har zuwa yanzu ba a ida tantance dinbin amfaninta ba,dukda yake yawan cin tafarnuwa kan sa mutum ya rinka warinta a dan haka sai a rinka ci akan ka'ida.
Ana soya tafarnuwa tamkar yanda ake soya albasa sai a rinka tarfawa ga abinci ko nama ana ci.

Tafarnuwa tana magance mahiyawan cutukan fata(cures a number of skin disease) kamar irin kurajen fuska sai a rinka gogata akan fuska bayan an tsageta.Ana yin haka na tsawon sati daya.
Tana maganin ciwon tari kamar na bronchities da masu fama da ciwon sanyin kirji (chest infection)

Tana maganin sanyin mara da ciwon sanyin mata a sabili da jima'i da mai ciwon (gonorrhoea).tana kuma maganin karamcin jini a saboda rashin cin abinci dan tana gyara miyau ta yanda hakan zai baiwa mutum damar cin abinci isashhe (appetite)
Tana karfafa garkuwan jiki dan yaki da cutuka da dama (immunity) 
ana baiwa kananin yara ita dan tana ba jikinsu kwarin guiwa da kuma kare 'yan cutukan dake yiwa yara karan tsaye.
Bugu da kari tana maganin cutukan zuciya dan takan rage yawan barazanar sinadiran cholesterol


Tana karfafa girman sababbin kwayoyin halitta (boosts the growth of new cells).
tana daidaita shuga a jiki

Post a Comment

0 Comments