A kullum ana fara ambaton a zaɓi mace ta gari a farko saboda
muhimmancin mace a cikin al’umma.Kowanne namiji yana fatan ya sama wa ‘ya’yansa
uwa ta gari ko da kuwa shi ya san halinsa yana da naƙasu.
Ya yin kuwa zaɓen mace ana son a samo ta gari duk lokacin kuwa da
aka sami akasin haka shi ke haifar da matsala ko bayan an yi auren. Wasu za su
iya cewa to me yasa matsalar ba ta hana auren ba?
Haka ne to amma me yasa matsalar ba ta hana auren mutuwa
ba?Dalilin da yasa hakan shi ne ƙaddara da kuma rufewar ido a soyayya ko kuma
girman wani ko wata makusanci ko wanda ya yi dalilin auren.Amma daga lokacin da
zama ya yi zama sai a fara tunanin neman mafita.Ta yaya maza za su gane mace ta
gari?
Mace ta gari ita ce ta siffantu da kakkyawar ɗabi’a da halaye da
kamala kallo ɗaya za a iya gane tarbiyyarta da ƙoƙarin da iyayenta suka yi
wajen ba ta tarbiyya.Mace ta kwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai
yi fatan a ce tana gidansa ta zame masa sanyin idaniya ta zama
al-mar’atissaliha da Annabi Muhammad (SAW) yace ta fi duniya da duk abin da
yake cikinta.Mace ingantacciya ita ce dai matar da kowanne namiji zai so ya
sami zuriya da ita.
Aure da dama a yau yana mutuwa amma sai a rasa dalilin mutuwarsa a
yi ta ɗorawa wani ɓangare na daban wanda wannan kuskure ne babba.
Abinda ya kamata a lura da shi shi ne in an bi ta ɓarawo sai a bi
ta ma bi sawu .
Maza suna da nasu naƙasun da rashin haƙuri amma kuma matan ma
akwai gyara a yadda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum a wani lokacin
yana saɓawa tarbiyyarmu ta Hausa/Fulani yana saɓawa al’adunmu da addininmu.
Bahaushe tun tasowarsa yana da tarbiyya da tsari managarci don yi
wa ‘ya’yansa tsani na samar da al’umma nagarta.Daga cikin abubuwan da mace ya
kamata ta zama don kama hanyar mace ta gari akwai:-
MAKAUNIYAR SOYAYYA
A duk lokacin da zafin soyayya ya ja ki ko dai ke don son da ki ke
yi wa mijin ko don shi son da yake ikrarin yana yi miki ko ma don a tunaninki
mallaka masa kan ki da ki ka yi shi ne matakin farko na wajibcin sai ya aureki
to kin yi kuskure.Maza ƙalilan ke iya wannan halascin ga mata.
Wasu matan ana yaudarar su ta hanyar kai kuɗin aure gidansu da an
kai sai iyaye su aminta da wanda ya kai kuɗin su sallama masa yarinya ita kuma
sai ta saki jiki wanda aure da dama da abin nema ya samu sai aure ya fara rawa
Kenan kuma ko da an yi auren wannan abinda ki ka yi sai a ƙarshe in aka yi
rashin sa’a ya janyo matsala duk kuwa da shi ne ma ya janyo hakan ta faru shi
ya yaudare ki ya yi miki romon baka.
KAMILALLIYA:
Mace kamilalliya it ace wadda take me kamun kai ba ta shiga
hayaniya z aka same ta ko da cikin ‘yan’uwanta mat aba ta da rawar kai bare a
gun maza .Kamilalliyar mace z aka same ta ba ta da shigewa maza ko da
muharramanta ne kullum in ka ganta da namiji da ya zama dole sai an gansu
saboda alaƙar karatu ko aiki ko wata hujja ta daban z aka ganta a tsorace tana
kaffa-kaffa.
In kuma ta sami wanda take so yana cikin matakin farko da mace ya
kamata ta fara nunawa a gun duk wanda take so su ƙullamu’amala take fatan
ɗorewarta zuwa aure.Hanyoyi da dama ya kamata mace ta bi don tabbatar da cewa
ita mai kamun kai ce.
Mata a yau a tunaninsu na yaudarasu don yadda suke ganin maza na
haba-haba da mata ba tare da nuna wani zaɓe ba to su sani iyakar ta waje ne
amma matar ta aure mai kamun kai ake nema.
SUTURA:
Sutura ita ce abin da ka sanya a jiki don kare tsiraici.Abu na
farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya gane ajin da zai ajiye ta shi ne
irin suturar da ta saka jikinta
Mata a yau suna tunanin bayyana tsiraicinsu shi ne hanyar da za su
iya janyo hankalin namiji gare su har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da
zai kai su ga aure.
Ko kuma wata wayewa ce da ci gabasaka matsattun kaya.Wannan babban
kuskure ne namjin da wannan zai ɗauki hankalinsa har ya yi tunanin ku yi sabo
to tabbas sai dai soyayya wanda a ƙarshe da-na-sani ne zai biyo bayan haɗuwar.
Macen da ke sanye da
suturar mutunci ake nema a aura ba ballagaza da ta gama nuna kanta a titi ba.
SURUTU
Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai macen kwarai ba a
santa da ɗaga harshe ba ko da a cikin ‘yan’uwanta mata ne bare kuma maza.Wata
matar tana tunanin in ta shiga dandazon maza ta ɗaga muryarta da zaƙewa shi ne
zai janyo hankalin namiji kan ta.
Mace mai kamewa da ƙarancin Magana tana da tasiri kwarai a lokacin
da ake batun aure da ma bayan an yi auren.Sau tari matsalar da ake samu na
shigar aikin assha tsakanin abokin miji ko kuma wani ɗan’uwan mijin tana fara
ƙulluwa ne ta yadda mace take sakin jiki ta yi ta surutu daga nan sai a gane ba
ta da tsada da an yi mata ƙaramar Magana za ta faɗa.
In kuwa haka ne to da sa hannun mata a yau wajen mutuwar aurensu
don duk auren da ba a yi masa ginshiƙi na kwarai ban a matar da za a aura akwai
yi wu war mutuwarsa.
0 Comments