Yadda Za Ka Gane Budurwa Bata Sonka Ko Yadda Za Ki Gane Saurayi Baya Sonki.

Yadda Za Ka Gane Budurwa Bata Sonka Ko Yadda Za Ki Gane Saurayi Baya Sonki.

1. Idan budurwa bata sonka bazata iya kiranka a waya da kud'inta ba, saidai tayi maka flashing, don haka iya mutuncin da zata iya maka kenan tayi maka flashin amma bazata taba iya kiranka a waya ba.

2. In budurwa bata sonka zata yi ta maka qorafi akan qananun buqatunta.

3. In budurwa bata sonka, zata yi maka wasa da dariya da murmushine kawai a lokacinda zaka bata kudi (money), kokuma a lokacinda take so ka bata kudi.

4. In budurwa bata sonka, bazata taba yi maka maganan aurenku da ita ba, ko maganan yadda tsarin aurenku takeso ya kasance ba.
5. In budurwa bata sonka, bazata taba rakaka wani waje ba, kudinda ita zata karba daga wajenka kawai tafiso.

6. In budurwa bata sonka, bazata ringa baka shawara akan rayuwarka ba, sannan bazata nemi kabata shawara akan rayuwarta ba.

7. In budurwa bata sonka, bazata taba kawo muku ziyara a gidanku ba.

8. In budurwa bata sonka, bazata taba gaya maka gasakiya akan labarin kanta ba, sedai tayita maka qarairayi.

9. In budurwa bata sonka,  bazata taba yarda ace kakarbi wayanta ka gani ba, saboda akwi lambobin samarikanta da yawa acikin.

Ko kun yarda da hakan?
In baka/ki yarda ba fadi tsokacinka/ki wajen comment.

Post a Comment

1 Comments