Takaitaccen tarihi na (Tahir Yusuf) Mai mallakin Lerawa Media Blog

 

   Assalamu Alaikum, da farko Suna na Tahir Yusuf, mahaifina sunansa Yusuf maihaifiyata sunanta Aishatu.
      An haifeni a ranar 18-09-1990 a cikin garin Lere, Lere Local Govt Kaduna State Nigeria, a garin lere na girma a shekara ta 1998 na fara karatuna a matakin firamare inda na shiga Dabo Muhammad Model Primary school lere, anan na fara daga aji daya (1) har zuwa ani shida (6). Shekara ta 2004
       A shekara ta 2004/2005 na shiga sakandire aji daya (1) watau jsss 1 knan, inda aji daya kawai na game daga Nan aka min taransifa (transfer) zuwa makarantar kimiya da fasaha dake garin Ikara a shekara ta 2005/2006 anan ne na game sakandire na a shekara ta 2010.
        Daga Nan na Sami admission a Kaduna State Cooperative Institute da ke garin Ikara a shekara ta 2012 zuwa lokacin da na game karatuna a matakin diploma, a shekara ta 2014 inda na karanta Information Communication Technology.
        Bayan gama karatuna na dawo gida, daga Nan kuma na Sami aiki a matsayin casual staff a gidan rafiyon jihar Kaduna a shekara 2015.
        A shekara ta 2018 kuma na nemi komawa karatu a matakin digiri inda na Sami admission a jami'ar jihar Kaduna (KASU) inda nake karanta Physics. A wata.
        A watan  7 na shekara 2018 kuma aka dauke ni aiki a matsayin cikakken ma'aikaci inda na koma hada hoto watau ( non-linear editor ko video editor) a turance.

AKARSHE
      Wannan shine tarihi na a takaice, ina godiya ga Allah da ya bani iko da lafiya ya kuma dakakani zuwa wannan matsayin, Sai Mamana da babana da Suka kala Dani har zuwa wannan lokaci, sai kawu na wanda shi ya nema min aiki, sai kuma dimbin masoya na da kuma yanuwada abokan arziki, naku har Kullum. Tahir Yusuf.
       Ku kasance tare Dani a kafafen sadarwa Kamar FacebookInstagram & Twitter 
Ina taya kowa murnar shiga sabuwar shekara.

Post a Comment

0 Comments