CIKAKKEN LITTAFIN KHAIRIYYA WANDA NANA FA'AD TA RUBUTA



Cigaban Khairiyya.
Da asuba ta tashi tayi sallah, ta d'au Qur'ani ta biya karatun jiya, bayan ta gama ta tashi taje fridge ta d'auka totolin ta shanye tas ta d'auka Roci ta tsosa, akasa ta zube tafara bacci kamar ba gobe sai kusan karfe takwas Haule tazo ta tashe ta
"Hajiya ki tashi ki shirya zakiyi lattin makaranta"
Khairiya tace cikin bacci "yanxu karfe nawa neh"
"Takwas hajiya, umm yi hakuri eight O'clock (8:00)
Khairiya batasan lokacin da ta tashi ba, cire kayan ta tafara agaban Haule, tace
"Haule cire mini uniform nawa, ki saka mini burger biyo da coke biyu a mota, socks nawa da takalmi na duk ki cire ki ajiye mini"
Tana fad'a ta shiga toilet tayi wanka cikin minti biyar tafito, mai ta shafa ta saka uniform nata, zama tayi tana shafa powder (huda) Haule kuma tana saka mata socks da takalmi a kafarta, bayan tagama tace Haule fito mini da jakata mota, takwas da rabi ta shiga mota ta zauna a ownest corner, d'aukan burger tayi tafara ci tana jiran driver yaja ta har tayi minti d'aya bataga driver ba
Fita tayi a motar tana ihun kiran Imran, amma shuru, dattijon nanne Garba yace
"Hajiya sai hakuri wlhy baiji sauki baneh shiyasa yau ma baizo ba"
Khairiya ta juya ta harare shi taja wani dogon tsoki tace
"Toh abakin aikin sa, kar na kara ganin sa a gida nah, nonsense" Garba na rokonta amma ku tsaya sauraran sa batayi ba
Shiga motar ta tayi ta fisga, kamar kullum tana gudu akan titi dan ita sam bata iya driving mota a hankali ba cikin minti takwas ta isa makaranta, karfe takwas maigadi yake rufe gate amma ita tana zuwa zai bud'e mata a kowani lokaci dan yasan halinta bata da mutunci kuma tana basa kud'i sosai
Shigan ta class malamin Biology neh a ciki, Corper neh (d'an bautan kasa)daga Imo state, sunan sa Christopher amma ana kiran sa da Corper Chris
Shiga tayi ba koh excuse,taku takeyi kamar batason taka kasa, kallo ya bita dashi sama da kasa yana had'e miyau, ya dakatar da ita yace
"Hea you, why do you come late"
Tana tafiya tace masa
"Issues"
Kallon mamaki yamata yace " what's your name" yana tambayar sunan ta
Sanda ta zauna akan kujeran ta tabaje kan tace
*" Kim"*
Yace "what type of name is this"
Batare da ta kalle shi ba tace "Meaning Khairiya Ibrahim Muhammad, my friends call me Kim that's in shortcut"
Yana lashe le6a yace "Kim Met me after class"
Ko ansa masa batayi ba, yana koyarwa tana d'an joter wa, dan Jamb saura sati biyu, bayan an tashi a makaranta aka basu hutu sai bayan Jamb su dawo, zata shiga motar ta kenan sai ga Corper Chris yace
"What happen i've been waiting for you in my office"
_(ya baki zo office nawa ba ina ta jiranki)_
Khairiya kallon kama raina ni ta masa tace
"Nincompoop kawai"she mumbled, ta fad'a a hankali kan tasake cewa
"ni zanje na sameka a office, Allah sawwaka, just tell me your problem now banda time da zan samei ka a office"
Ba abun da yaji sai just tell me your problem, abun bai masa dad'i ba amma she's too hot to ignore bazai iya barin taba, yana murmushi yace
"Amm I just wanna say you are Hot"
Tsoki taja ta kallesa sama da kasa tace
"I know m HOT, u don't have to say it"
Corper Chris yana lashe baki yace
"Emm I want you to come to my house, so that we can catch some Fun"
Sarai tasan mei yake nufi, tufar da miyau tayi ta kalle sa, kallon tsana tace
"Kai amma Allah ya'isa tsakani na da kai, ni mazan larabawa da Indiya wa ma basa burgeni balle kai inyamuri, kama cuce ni ka raina ni wlhy, bari zan koya maka hankali" ta fad'a tana murmushi
Duk abun da take fad'a bai jiba, amma yasan bata amince ba, yace "I dnt get you Kim what do you mean"
_(Ban fahimce kiba Kim)_
Murmushi Khairiya tayi tace
"Dont worry Chris, just give me your address, tomorrow is Saturday right?, Expect me in d Morning around nine, I'm gonna spend the whole day with u, I love catching Fun, catching Fun is my favorite"
Wani shu'umin murmushi yayi, mika masa takarda da biro khairiya tayi tace "write it down, I mean your address"
Kar6a yayi ya rubuta mata har number wayan shi, yace
"What do u want me to keep for you"
Tayi murmushin mugunta tace
"You, I just want you en nothing else"
Wani dad'i yaji kamar ya kashe shi, sai godiya yake mata, ta hau motar ta ta fisge shi, tana barin haraban Makarantan Wayar ta ta kunna ta latsa numban Kamalu bad (shineh da yaransa suka ma Zil duka a shopping mall), Kamalu badd sunan da ake kiran shi kenan, shineh babban su a 'yan ta'adda
Kamalu badd na d'aukan wayan Khairiya tace
"Akwai aiki tomorrow in the morning, kazo around nine kaji, kar kaje kana mini shirme kace baka ganeh time ba, what I mean is kazo kafin Tara na safe" koh jiran ansa batayi ba tayi hanging call d'in Tana shiga gida tayi parking na motar ta a parking space, tafita a motan ta taji murya ta bayan ta ana cewa
"Queen Khairiyya daughter'n Abba ya makaranta" wani dattijo neh dogo bak'i kyakkyawa yana murmushi
Tura baki Khairiyya tafara tace
"Ni ba ruwana da kai ai Uncle Hisham, tun da katafi Lagos sau d'aya ka kirani, ka manta dani gaba d'aya"
Wanda takira da Uncle Hisham yace
"Haba khair kinsan aikin mu ba Hutu, kuma ke kullum kin cika canje canjen number"
Tayi murmushi tasan yana da gaskia dan a wata sai ta canza Sim card sau biyu wani sa'in sau uku ma, tace
"Toh naji Uncle, yanxu ina tsaraba ta"
"Haba khair baza mu shiga ciki mu zauna ba kina maganar tsaraba"
Tana kumbure kumbure tace "toh mushiga"
Suna shiga parlour Uncle Hisham ya zauna ita kuma tashiga kawo masa kayan motsa baki, gaban shi dam ta ciki dasu snacks da drinks, ba abun da yasha sai Malt, ya d'an sha kad'an yace
"Khair Sarauniya, nazo na d'auke ki muje gida nah kiyi koh wata d'aya"
Khairiyya tana washe baki tace
"Laa Uncle Yaa Ammar yadawo neh"
"A'a bai dawo ba Khairiyya sai nan da wata shida"
Ta tura baki tace "gaskia Uncle Hisham Abba ma yace na zauna a gida baya so ana barin gidan ba kowa empty" a zuciyarta sai cewa take Tab naje gidan ka Matar ka ta hanani sakat ana zaune kalau, da Yaa Ammar yana nan neh ma toh zan iya zama amma shima bayanan ga gobe akwai catching Fun na bika Kut ai bazai yuba
Uncle Hisham yace "Haba Khairiyya yanxu kina jin dad'in zama Ke d'aya daga ke sai masu aiki, kina yarinya karama wannan wace irin rayuwa ce ehh"
Hawaye tafara tace "Uncle Hisham tun ina karama nake living like this miserably, ina garin da kake aiki can mahaifiya ta take, wannan maganar kuma ba ni yakamata ka mini ba Ammi ce yakamata ka mata, ita tabar loneliness helpless child"
Shiga d'akin ta tayi da gudu ta kulle kofa tana kuka sosai, wani irin iyaye Allah ya had'a ta dasu, gwara Abban ta tasan dalilin neman da yakeyi,and she cant stop him amma Ammi fa, taje tana jin dad'in rayuwar ta ta manta dani"
Tun Uncle Hisham na buga kofa har yagaji ya bar gidan, tana jin motar shi yabar gidan tayi sallah Zuhur tayi Asr, abinci ma ta kasa ci, tun da nazo duniya da 'yan aiki nake rayuwa, wannan wace irin rayuwa ce wai take fad'a da ihu
Kofan d'akin ta ake bugawa, Khairiyya tace
"Who the hell is knocking my door"
Dije ce a kofan tace
"Hajiya abincin ki na kawo miki"
Khairiyya ranta ya kara 6aciwa dan idan ta shiga cikin damuwa batason kowa ya mata magana, tace
"Dan kaniyar ki yar shishshigi ni nace ki kawo mini abinci, toh kije bazan ciba"
"Haba Hajiya dan Allah"
Wlhy idan na fito ranki zai 6aci kibar mini kofa nace, ta fad'a a tsawace, hakan yasa Dije ta bar wajen
Khairiyya bud'e fridge nata tayi tasha codein da benelyn kwal6a biyu kan taji daidai, zubewa tayi a kan babban gadon ta wanda zai iya d'aukan mutaneh biyar tafara bacci, itace bata farka ba sai karfe bakwai daidai ana kiran sallar Magrib, da kyar ta iya yin sallah tsaban yunwan da takeji, rabuwar ta da saka abu a baki tun burger na safe
Dining taje taga empty, Haule ce kawai take kwana
a gidan, kiran Haule tayi da muryan da Allah ya bata da karfi, Haule tazo ta durkusa tace
"Na'am hajiya ganinan"
"Wai uban mei kikeyi a ciki inata kiranki sai yanxu kikaga daman fitowa" cewar Khairiyya
"Hajia Wlhy kina soma kirana koh second ban karaba na fito"
"Ahh toh sharri na miki koh, Haule ki amsa mini na d'aura miki sharri kike nufi koh"
Haule ta sunkuyar da kai tace "Hajiya kiyi hakuri ba hakan nake nufi ba dan Allah"
Tsoki Khairiyya taja tace "Mei Dije ta girka"
"Hajiya Shinkafa da wake da miyan ja"
Wani kallo Khairiyya ta watsa mata wanda yasa har cikin Haule yayi kuka kuuu, Haule muryan ta na rawa tace
"Yi hakuri Hajiya Rice/Beans with stew"
Khairiyya tayi jimm, ta fusgar da iska tace
"Amma lalle Dije ta raina ni, sau nawa zan gaya mata bana son kayan tusa, musamman da daddare, cikin mutum ya 6aci inje inata tusa ina shigan toilet ba gaira ba dalili, mtseww kuma Wlhy yunwa nakeji"
Haule tace "Hajiya koh zan dafa miki wani abincin neh"
"Ai toh Haule da kin iya dafa abinci bazan tsaya ina 6ata lokaci nah ina miki dogon zance ba, your food makes me puke, kawai had'a mini G&G ki kawo mini banson stew"
Haule a zuciyarta cewa take ai gwara ni ina kokarin abincin kefa, tsawan da Khairiyya ta mata shi yadawo da ita da maganan zucin da takeyi
"Tunanin Uban mei kikeyi neh Haule, idan tunanin saurayi neh toh Allah sawwaka nidai kije ki had'o mini abinci" Khairiya ta fad'a a tsawace
"Umm Hajia yi hakuri naji kamar kince G&G ni kuma bansan abincin ba balle na girka" cewar Haule
Kai kai Yaa Salaam, wai ni Abba da wani irin villagers masu aiki ya had'a ni dasu neh, toh abincin kauyen ku wanda kukeci kullum, abun da nake nufi Shinkafa da wake yi mini had'in garau garau dashi yi sauri inajin yunwa"
Haule ta tashi tayi hanyan kicin sai cewa take Allah shirya Khairiya garau garau ma baza ta iya fad'a ba sai G&G taja tsaki
Bayan Haule ta had'a mata garau garau nata taci tayi nak, tayi alwala tayi sallan Isha'i, wayan ta ta d'auka ta kira Abba,
"Abba yau throughout baka kirani ba fa" ta fad'a tana tura karamin bakin ta
Abban yace "wollah Mamata i've been trying your line d'azu but baya shiga, yakike ya shirye shiryen Exams"
Tace "Abba gaskia karatu da wahala kuma jamb wani sa'in ba karatun ka baneh a had'e da sa'a kayi wani abu dan ni inason next section nashiga jami'a"
Abba yace "Khairiyya kiyi karatu kinji, In Shaa Allah zaki ci, now kiyi bacci you need to rest"
"Ohk Abba sai da safe gudnyt" ta katse wayan
Mallam Ali baizo yau ba,dan haka shiga su Snapchat da Instagram tayi, bayan tayi dube duben ta, tayi addu'a ta kwanta bacci
Washegari da safe bayan tayi sallan Asuba ta kwanta bacci ita bata farka ba sanda wayan ta ya damei ta da ringing, d'aukan wayan tayi batare da duba wanda ya kira ba, taji ana cewa
"KIM muna kofan gate na gidan kifa tun d'azu ina kiranki bakya picking"
Cikin muryan bacci "tace Kamalu badd yanxu karfe nawa"
Yace "Kim yanxu Tara da rabi fa"
A take ta tashi tace "Toh ka bani 30mins zan fito kaji"
Yace ba damuwa KIM koh nan da awa d'aya neh mu masu jiranki neh
A gaggauce ta fad'a toilet tayi wanka, dining taje taci abinci dan sauri ma bata tsaya cin mutuncin Dije ba yau ba, bayan ta gama ci ta shiga d'akinta ta saka wani dogon rigar yar kanti armless (ba hannu)mei kala red da black, ta saka jacket baki akai tayi rolling da gyale red, simple makeup tayi yau daga powder sai lipgloose da mascara,da wani Red takalmi mei uban tsayi, d'aukan paper da Corper Chris ya bata tayi ta fita parking space ta shiga motarta taja wajen gidan, a waje bakin gate nata ta gansu Kamalu badd suna zaune acikin motar su Odesys, Kamalu badd yana ganin ta ya fita a motar, yazo dab kusa da motar ta ita kuma ta sauke Glass, yace
"KIM wani aiki neh haka"
Khairiyya tace "wani neh nakeso mu d'an koya masa hankali"
Kamalu badd yace "Hajiya KIM an gama, wani anguwa neh"
Ba tare da tace komai ba ta cire paper da Corper Chris ya bata ta mika masa, Kamalu badd yace
"Haba KIM kinsan ni ban iya abun ku na boko ba kawai karanta mini"
Batare da tace komai ba ta bud'e paper ta karanta _shagari low cost house A no34_ ga number wayan shi akasa
Kamalu badd ya bud'e baki yace "Kutt KIM, kinsan Shagari lowcost anguwan soldiers (sojoji)neh koh, kuma gaskia bazan 6oye miki ba tsoron sodoji muke,ga 'yan anguwan sunsan bariki basa tsoro, kafin a shiga anguwan ma suna checking kar su kama mu tun a gate
Dariya Khairiyya tafara tace
"Kai ban ta6a sanin kana da tsoro ba sai yau, amma ka bani kunya Wlhy, kar kaji komai zamu sake musu kud'i idan kud'i batayi aiki ba ma gubza dasu, balle ma nasan cash zaiyi aiki, shiga motar ku kawai mu tafi"
"Angama Hajiya KIM"
oper Chris,
Hanyan Shagari lowcost suka kama, nan da minti goma suka isa dan gudun da sukeyi, a bakin gate wasu sojoji neh sun saka bak'in glass fuskarsu a murtuke kamar wanda aka musu mutuwa, Khairiyya ce a gaba su Kamalu badd a bayan ta, Glass na motar ta ta sauke, wani bak'in soldier neh yace fito ki bud'e boot naki, ba musu tafita tana tafiyar ta mai d'aukan hankali ta bud'e boot nata, dubawa yayi yaga ba komai sai spare tyre, duk sojojin kallon ta suke dan Khairiyya ta d'auke musu hankali, sojan murmushi yayi yace
"Baby mei sunan ki"
Tana mai mayar mishi da murmushi tace "KIM"
Yace "Wow nice name, you are so beautiful"
"I know " shineh kawai abun da ta furta tashiga motar ta, sojan nan haka ya bita yace
"Ki tsaya muyi magana mana"
Khairiyya tana mei kallon sa ba yabo ba fallasa tace
"Dont worry yanxu ina sauri yayata tace na kawo mata carpenters kaga suneh a bayana so please ba sai ka duba suba idan zamu fita zan tsaya muyi magana handsome"
Kiran shi handsome da tayi ba karamin dad'i ya mishi ba, sai washe hakura yake kamar mai tallan close up yace
"Ok ok no problem I will be here waiting"
Tace alright then sai mun fito, ta fisga motar ta ciki su Kamalu bad suka bi bayanta, Line A yana can ciki ciki haka dai suka shiga, suna duba koh wani numban gida, dan kowani gida an rubuta numban a waje, suka samu A36 suka zagaya sukaga A34
Wayan ta ta cire ta latsa numban shi, ringing d'aya ya d'auka wayan
Khairiyya tace
"Hello Corper Chris it's me KIM"
Daga can Corper Chris yace "Ohh the damsel Kim, i've been waiting for you since, where you at"
Khairiyya tayi murmushin mugunta tace "At the door sir, can I come in"
"Sure Damsel Come In, fell free dear"
Tace "ohk"
Ta katse wayan, juyawa wajen su Kamalu tayi tace ku shiga bayan minti d'aya, suka ce an gama Kim
Tura kofan tayi ta shiga, ba laifi gidan tsab sai d'an warin toilet da yake tashiwa, washe hakora yake yana cewa
"Welcome Damsel, welcome"
Ya bud'e mata hannu alaman ta rungume sa
Kau da kai tayi tace "I am tasty"
"Ohhh sorry pls lemme offer you drinks but before then have a seat" nuna mata kujera yayi ta zauna ya bud'e fridge ya ciro faro water da Coke na roba, kan ya ajiye a gaban ta su Kamalu suka shigo gidan
Corper chris sai ganin maza karti yayi akan sa da kayan aikin su, muryan sa na rawa yace
"Who are you, What do u want? "
Kamalu neh ya amsa yace
"Uwaka da Ubanka neh"
Khairiyya ta fashe da dariya Coper chris ya juya yana kallon ta with suprise on his face yace
"Why Kim, Why? "
Dariyan ta tacigaba tace
"Ohhh Corper Chris you love catching Fun right, we gonna catch some fun now"
Muryan sa yana rawa yace "what do u mean by that, Please Kim I beg of you don't do anything stupid"
Su Kamalu bad da yaransa suma sai dariya suke masa dan kusan duka basuji mai suke cewa ba
Zaiyi ihu Kamalu ya kai masa bugu bakin sa, Khairiyya tace
"Ahswear Chris don't you dare try that, bamu fara catching fun ba but you are already looking like a fish who has mental issues, ohhh you are such a frickle doodle"
D'aura shi sukayi da igiya mai karfi hannun shi da kafan shi, gum mai karfi suka manna bakin shi dashi
Khairiyya tace "Wow I'm gonna enjoy this"
Shiko duk an d'aure shi ga baki an toshe ba abun da yakeyi sai hawaye
Dukkan su dariyan sa suke Khairiyya tace
"We ain't even started, save your tears for letter durling"
Zuwa wajen fridge nasa tayi ta d'auko ruwa masu sanyi ta watsa masa a jikin sa, sai shure shure yakeyi, gashin kansa daman yatara gashi irin na gayu Razor Kamalu bad yacire sabowa yasaka sabulu da ruwa akansa yafara masa aski, gabad'aya yabi ya 6ata masa kansa kaca kaca
Wani k'aton bulala Khairiyya ta d'auka ta fara zane shi da bulala tana cewa
"Ohhh I love this, this is fun, no more than that, ohhhh" sanda hanun ta yagaji ta barsa, tace Kamalu mu barsa haka atleast yayi catching Fun yanxu, kuma nasan bai ta6a catching Fun irin na yau ba en it will stuck in his brain forever
Corper dai sai hawaye dan kuka ma bazai iyayi ba dan an rufe bakinsa,Khairiyya tace
"Tell nobody, Idan kafad'a hmmm i'm gonna rip off your head en then feed it to your bitches" taja tsoki
Khairiyya da mutanen ta suka barshi a wajen suka shiga motar su, fitan su a gidan wani yagansu ya shigo da gudu yaga Chris a d'aure, neman wuk'a yayi ya kunce sa ya bud'e masa baki, yace
"Brother Chris what happen"
Kasa magana yayi Chris sai neman wayan sa da yake, yana samuwa ya danna wani numba an rubuta my brother, latsa number yayi yakira
Ana d'aukawa Chris ya fashe da sabon kuka yace
"Broh m finished, some people came en beat me up, don't allow them out of the gate pls broh, don't let them go" ya kara fashewa da kuka dan yaji zafin dukan da Khairiyya ta masa, ga naushin da Kamalu yamasa sanda bakin sa ya fashe
Yayan yace "what type of car Chris"
Chris yace "i don't know lemme ask Gabriel"
Ya juya wajen Yaron da ya taimaka masa yana hawaye yace
"Abeg Gabriel what type of car do you see them with"
Wanda aka kira da Gabriel yana d'an tunani kan yace
"Yes the guys with Odesys en the babe with S-Cross"
A take ya fad'awa yayan nashi, yayanshi d'aga kai da zaiyi ya kalla motan sun kusan zuwa gate d'in, a take ya tashi yana ihu yana cewa
"Don't let them out" da karfin sa, duk sojojin suka tashi suka tsaya bakin gate d'in sukayi cracking gun (gyara bindigansu) hankalin su atashe duk a zaton su an kawo musu attack neh
Su Khairiyya sai gani sukayi sojoji sun seta bindiga akansu, gaba d'aya sun tsorata

Akace laifin dadi karewa, anan zamu tsaya sai wani lokacin.
   Me tambaya ko karin bayani ya yayi comment a kasa da tambayarsa ko karin bayaninsa.
 Naku Tahir Yusuf  Nagode.

Post a Comment

0 Comments