==========================
Ana Bukatar Jama'a su yada wannan Post zuwaga Sauran Al'umma domin Qaruwa da Juna.
1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).
2- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.
3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko
wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.
4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
5- Ana sanya garin zogale akan wani
rauni ko gembo domin saurin warkewa.
6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.
7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa
kanwa 'yar kadan domin maganin ciwon
shawara.
8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan
danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.
9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
10-Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale
da citta kamar shayi.
.
11-Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin
sanyi.
.
12-Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.
.
13-Ana daka ganyen zogale da 'ya'yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin
ciwon hanta.
.
14-Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya 'ya'yan zogale a daka su
sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
.
15-A daka zangarniyar zogale da 'ya'yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji
da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.
.
16-A daka saiwar zogale da 'ya'yan
kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).
.
17-Haka kuma idan mutum yana
fama da ciwon Aids zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.
.
18-Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.
Allah ya sa mu dace
0 Comments